IQNA

An Kaddamar da Cibiyar Musulunci a Wales, UK

22:54 - December 14, 2021
Lambar Labari: 3486685
Tehran (IQNA) An kaddamar da Masallaci da cibiyar muslunci ta Abergavenny da Islamic Center a Wales, UK tare da halartar magajin gari.

Tudor Thomas, magajin garin Abegon, ya yi matukar maraba da bude masallacin da cibiyar musulunci, ya kuma jaddada cewa al'ummar Wales suna zaune lafiya da dukkanin mabiya addinai da al'ummominsu, yana mai cewa kasancewar cibiyar musulmi a Wales yana nufin cewa al'ummar musulmi su ne jigo ne a rayuwarsu, Ayyukan zamantakewa da al'adunsu a yankin.

A baya dai an baiwa al'ummar musulmin Abargoni damar gudanar da sallar Juma'a a birnin.

A wajen bikin, Musulman birnin sun bayyana shirinsu na karbar 'yan gudun hijirar Afghanistan.

Abergoni gari ne na kasuwanci a cikin Wales, yana cikin yankin Monmouthshire, yana da yawan jama'a kusan 12,000.

Akwai masallatai kusan 40 a Wales, kuma yawancinsu an gina su ne a garuruwa irin su Cardiff da Newport da Swansea, wadanda ke da yawan musulmi. Wales tana da Musulmai kusan 50,000.

 

 

 

4020552

 

 

 

 

captcha