IQNA

Hizbullah Da Amal; Fayyace Gaskiyar Lamari Kan Fashewar Beirut Ya Dogara Da Yadda Alkalai Suka Bi Tsarin Mulki

18:06 - December 16, 2021
Lambar Labari: 3486691
Tehran (IQNA) Hizbullah da Amal sun fitar da bayani na hadin gwiwa kan batutuwa da suka shafi halin da ake cikia kasar Lebanon a kan batutuwa daban-daban, na siyasa, tsaro, tattalin arziki da sauransu.

Shafin Al-ahad ya bayar da rahoton cewa, Shugabanin kungiyar Amal da kungiyar Hizbullah a cikin wata sanarwa da suka fitar bayan wani taron hadin gwiwa da wakilansu na yankunan  kudancin kasar Lebanon, sun jaddada muhimmancin bin dokokin da ke cikin kundin  tsarin mulkin ga alkalai, domin samun adalci da kuma fayyace gaskiyar lamarin da ya faru a tashar jiragen ruwa ta Beirut.

Ban da wannan kuma, kungiyar Amal da Hizbullah sun fitar da sanarwar hadin gwiwa, inda suka yi tir da tabarbarewar harkokin kudi, tattalin arziki da rayuwar al’umma a kasar Labanon, tare da yin kira ga hukumomin tsaro da na shari'a, da ma'aikatun da abin ya shafa da su dauki matakin rage kuncin rayuwa ga al'ummar kasar.

Kamar yadda kuma suka bukaci da a daukai matakai na gagaguwa a bangaren hada-hadar kudade, don magance hauhawar farashin kudaden waje, wanda yake yin mummunan tasiri a kan tattalin arzikin kasar, da kuam magance matsalar samar da magunguna, abinci da sauran bukatun jama’a.

Wakilan kungiyoyin Hizbullah da Amal a cikin sanarwar, sun jaddada aniyarsu ta bin kundin tsarin mulkin kasa day a tanada kan kan dokokin zabe, da kuma gudanar da zabuka a kan lokaci, tare da yin kakkausar suka ga duk wani yunkurin dage zaben ko kuma kawo cikas ga shirin.

A cikin bayanin nasu, sun kuma yi kira ga kungiyoyin Palastinawa da su yi taka tsan-tsan tare da kauracewa fadawa tarkon rarrabuwar kawuna, suna masu jaddada cewa babban abin da ke gaban kungiyoyin Palastinawa shi ne tsayin daka wajen tinkarar mamayar da yahudawan sahyoniya suke yi wa kasarsu ta Falastinu.

A karshen wannan sanarwa, ta kungiyoyin Amal da Hizbullah ta  jaddada karfafa hadin kai a tsakaninsu a matakai daban-daban na jagoranci, bin tsari a dukkanin bangarori, musamman a zaben 'yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi, da kuma fuskantar matsalolin zamantakewa da tattalin arziki, domin tabbatar da ‘yancin kasar Lebanon da al’ummarta.

 

4021235

 

captcha