IQNA

Barazanar Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda A Gabashi Da Kudancin Nahiyar  Afirka

12:46 - December 19, 2021
Lambar Labari: 3486701
Tehran (IQNA) Kasashen gabshin nahiyar Afirka sun shiga cikin cikin kasashen da ke fuskantar barazana daga kungiyoyin ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi.

A ranar 16 ga watan Nuwamban 2021 ne dai kungiyoyin ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi suka kaddamar da wasu munanan hare-haren bama-bamai a cikin birnin Kampala fadar mulkin kasar Uganda, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku da kuma jikkatar wasu da dama.

Wadannan hare-hare dai suna zuwa ne a  daidai lokacin da kungiyoyin ‘yan ta’adda suke kara zama babbar barazana ga yankunan gabashi da kuma kudancin nahiyar Afirka.

Harin na birnin Kampala dai an kai shi ne da rana tsaka a lokacin da mutane suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum, da hakan ya hada da wuraren ayyukan hukumomin tsaro da ma’aikatu na gwamnati, amma jami’an tsaro sun bayyana cewa sun gano wadanda suka kai harin na kunar bakin wake, kuma dukkaninsu musulmi ne.

Wannan ya sanya hukumomin na Uganda suka fara  nuna yatsan tuhuma  akan musulmin kasar wadanda su ne marasa rinjaye, lamarin da ya sanya musulmin kasar a cikin fargaba, domin kuwa jingina ayyaukan ta’addanci a  gare su, na nufin daukar matakai na takurawa a kansu, da ma yiwuwar hana su gudanar da wasu harkokinsu na addini, ko kuma kafa musu wasu sharudda masu tsauri.

To sai dai musulmin kasar ba su yi wata-wata ba wajen yin Allawadai da wannan hari, tare da nisanta kansu da wadanda suka kai shi, da kuma tabbtar da cewa duk wanda yake da hannu a  cikin wannan hari, ko da ya kira kansa musulmi, to baya wakiltar musulmin kasar ko kuma addinin muslunci, yana wakiltar kansa ne kawai.

Baya ga haka kuma wasu daga cikin kungiyoyi da jam’iyyun siyasa ma sun nuna rashin gamsuwa da bayanin gwamnatin kasar Uganda na dora tuhuma a kan musulmin kasar, daga cikin wadanda suka ki amincewa da wannan tuhuma a kan musulmi kuwa har da babbar jam’iyyar adawa ta kasar ta FDC.

Kakakin jam'iyyar ta FDC ya yi wani taron manema labarai a birnin Kampala bayan faruwar lamarin, inda ya yi gargadi game da jingina wa musulmi alhakin hare-haren ta'addancin da aka kai a kasar, yana mai cewa al'ummar Musulmin Uganda na cikin firgici kan zarginsu da hannu a hare-haren ta'addancin na baya-bayan nan.

Kakakin jam'iyyar FDC Ibrahim Ssemujju Nganda, ya bayyana cewa, ana ayyana masallatai a matsayin cibiyoyi na masu tsattsauran ra'ayi kuma akwai fargabar cewa jami'an tsaro za su fara kai hari a wuraren ibada na musulmi.

Da yake sukar kalaman shugaban na Uganda da ya yi kan batun kai harin, ya ce: “Yuri Mosivini ya zama mai fassara addinin Musulunci, Yana daukar kansa kwararre wanda ya san koyarwar addinin musulunci, to dole ne ya dakatar da wadannan maganganun.

A cikin jawabinsa na karshen mako Mousevini ya ce wadanda ke da hannu a ayyukan ta'addanci suna da sunayen musulmi ne, yana mai kokarin danganta harin ta'addancin ga musulmi.

Nganda ya ce: "Hari kan masallatai, kama mutanen da ke zuwa makarantun addini wani nau'i ne na wariya." Wajibi ne hukumomin tsaro su yi taka-tsan-tsan wajen tunkarar wannan matsala.

Rundunar ‘yan sandan Uganda ta tabbatar da cewa an kashe ‘yan ta'addar da suka kai hare-haren, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano dukkanin wadada suke da hannu a cikin lamarin, domin su fuskanci hukuncin da ya dace da su.

Wannan lamari da ya faru a kasar Uganda, ya sanya sauran kasashen yankin shiga cikin firgici, da kuma yin tunanin yadda za su kara karfafa hadin gwiwa  a tsakaninsu domin fuskantar wannan barazana ta ta’addanci, inda ‘yan kwanakin bayan kai harin na Kampala, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya kai wata ziyara a kasar Afirka ta kudu, inda ya gana da takwaransa na kasar Cyrill Ramaphosa a kan wannan batu.

Ramaphosa ya ce kungiyoyi irin su ISIS da suka kai hari a kasashen Afirka irin su Mozambik da Uganda, za su iya isa Afirka ta Kudu.

Shugaban na Afirka ta Kudu ya ce ba za a taba yin watsi da barazanar masu tayar da kayar baya ba, domin kuwa burin irin wadannan kungiyoyin shi ne tayar da hankulan jama’a da hana kasashe zaman lafiya.

Ramaphosa ya ce, Wadannan kungiyoyi da suka zo da sunaye daban-daban suna da hadin gwiwa a tsakaninsu wajen gudanar da ayyukansu na ta'addanci, Saboda haka, a matsayinmu na kasashen nahiyar Afirka, dole ne mu dauki matakan da suka dace ta hanyar hadin gwiwa tare da hada kai wajen musayar bayanai, yin aiki tare, da kuma bin diddigin wadannan 'yan ta'adda a duk inda suke.

Ya ce Kungiyar ISIS dake gudanar da ayyukanta na ta’addanci a kasashen Muzambik da Uganda da kuma gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, ta yi barazana a shekarar da ta gabata cewa, za ta dauki mataki kan duk kasar da ta tura sojoji zuwa Mozambique domin yaki da su, wanda hakan a cewar Cyrill Ramaphosa ishara ce ga kasar Afirka ta kudu, wadda ta tura sojoji zuwa Mozabique domin taimaka wa gwamnatin kasar wajen tabbatar da tsaro da kuma yaki da ‘yan ta’adda.

A cikin watan Yulin da ya gabata, sojojin Afirka ta Kudu da wasu kasashen yankin suka shiga birnin Cape Delgado (arewacin Mozambique) domin yakar kungiyar ISIS a wani bangare na ayyukan tabbatar da tsaro na rundunar sojin kasashen kudancin Afirka (SADC).

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana damuwarsa matuka dangane da karuwar barazanar ayyukan ta’addanci na irin wadannan kungiyoyi, musamman kasar Kenya wadda take makwabtaka da Somalia, wadda kuma take fuskantar irin wadannan ayyuka daga kungiyar Al-shabab ta Somalia, wadda ta kai munanan hare-hare a  cikin kasar Kenya a lokuta daban-daban.

A kan haka ya ce, dukkanin kasashen yankin gabshi da kudancin Afirka dole ne su hada karfi da karfe domin yin aiki tare, da nufin kawo karshen kungiyoyin ‘yan ta’addan a yankin baki daya.

Haka nan kuma shugabannin na Afirka ta kudu da Kenya sun yi Allawadai da kakkausar murya dagane da harin da aka kai a kasar Uganda, tare da jaddaa cikakken goyon bayansu ga al’ummar kasar.

Sai dai bayan kammala wannan ziyara ta Shugaban kasar Kenya a kasar Afirka ta kudu ke da wuya,  Kungiyar ‘yan ta’adda ta Alshabab a kasar Somaliya ta dauki alhakin tayar da bam a wata makaranta a tsakiyar birnin Magadishu babban birnin kasar ta Somalia, wanda kuma ya yi sanadiyyar mutane 8 daga ciki har da wasu ‘yan makaranta.

Kakakin rundunar ‘yansanda a birnin Magadishu Abdulfatah Adam Hassan ya ce, banda mutane 8 da suka rasa rayukansu akwai wasu 17 wadanda suka ji rauni.

Kungiyar ta Alshabab ta bada sanarwan daukar alhakin harin ne ta tashar radiyonta wacce ake kira ‘Andulos’. Ta kuma kara da cewa tana nufin kai harin ne kan wasu jami’an gwamnatocin kasashen yamma, wadanda suke ziyara a kasar, kuma wadanda sojojin tarayyar Afrika suke bawa kariya.

Wani mutum wanda yake inda abin ya faru ya sheda cewa jami’an tsaro masu zaman kansu ne suke bawa bakin kariya a lokacin da bom din ya tashi, sannan ya ga mutane 4 daga cikin jami’an tsaron sun ji rauni a harin.

Masana kan harkokin tsaro da na siyasa sun yi imanin cewa, barazanar ayyukan ta’addanci a wadannan yankuna abu ne mai matukar daga hankali ga al’ummomin yankin, musamman ma kasantuwar cewa akasarin kasashen kudancin Afirka da ma wasu kasashen yankunan gabashin Afirka ba mabiya  addinin muslunci ba ne, wanda hakan zai iya sanya wa cikin sauki su iya dora alhakin hakan a kan musulmi, alhali kuwa ayyukan irin wadannan 'yan  ta’adda a duniya, yafi karewa  ne akan musulmi, domin kuwa kasashen da suka fi yi wa illa kasashen musulmi ne, inda kuma  nan suka fi kashe mutane.

Misalin hakan shi ne kasar Syria, da kuma Iraki, Afghanistan, inda kusan illahirin mutanen da wadannan ‘yan ta’adda suke kashewa a wadannan kasashe musulmi ne.

Kamar yadda kuma za a  iya bayar da misali da Najeriya, inda a can ma akasarin hare-haren irin wadannan ‘yan ta’adda sun fi karewa ne a kan masallatai da kasuwanni da wuraren hada-hadar jama’a, kuma dukkanin hare-harensu suna karewa a arewacin kasar a biranen musulmi, kamar yadda haka lamarin yake a Mali da Chadi da Burkina Faso Da kuma Jamhuriyar Nijar.

Wanda kuma ko shakka babu, kisan gillar da wadannan ‘yan ta’adda suke yi wa musulmi a kasashe daban-daban da sunan jihadi, shi kadai ya isa ya tabbatar da cewa manufarsu ba ita ce daukaka addinin muslunci ba kamar yadda suke ikirari, bil hasali ma suna bakanta sunan addinin muslucni ne, kuma suna nisanta kansu daga sahihiyar koyarwa ta addinin musulunci, wadda ta ginu a kan girmama ra’ayin juna, da mutunta juna, da tausayin dan adam da karrama shi, da kuma kare rayuwarsa da mutuncinsa, da zama lafiya da kaunar juna a tsakanin dukkanin mabiya addinai.

 

By:  Abdullahi Salihu Usman

 

 

captcha