IQNA

Aljerya Ta Mika Nasarar Da Ta Samu A Wasan Kwallo Na Kofin Kasashen Larabawa Ga Al'ummar Falastinu

17:47 - December 19, 2021
Lambar Labari: 3486703
Tehran (IQNA) Mai horar da 'yan wasan kasar Aljeriya ya mikawa al'ummar Palastinu musamman al'ummar Gaza nasarar gasar cin kofin kasashen Larabawa.

Shafin yada labarai na Al-ahad ya bayar da rahoton cewa, tawagar kwallon kafar Aljeriya ta lashe wasan farko na gasar cin kofin kasashen Larabawa da Qatar ta karbi bakuncinsa a yammacin ranar Asabar, inda ta doke Tunisia da ci biyu.

Kocin tawagar 'yan wasan kasar Aljeriya Majid Bougreh ya mika wa al'ummar Falasdinu nasarar da suka samu a wasan, inda ya ce hakan abin alfahari ne a ga al'ummar Aljeriya baki daya.
 
A yayin gasar, dukkanin magoya bayan kungiyoyin kwallaon kafar na kasashen biyu Aljeriya da kuma Tunisia, sun yi ta rera take nuna goyon bayansu ga al'ummar Falastinu, a matsayin sako na nuna rashin amincewa da kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra'ila da wasu gwamnatocin kasashen larabawa suke ta hankoron yi.
 
Bayan kammala wasan dukkanin mahalarta wurin sun yi ta rera taken nuna goyon baya ga Falastinu da masallacin Quds, tare da daga tutocin Aljeriya da Tunisia da kuma Falastinu a lokaci guda.

تقدیم قهرمانی تیم ملی الجزایر به مردم فلسطین

تقدیم قهرمانی تیم ملی الجزایر به مردم فلسطین

 
 
captcha