IQNA

Lebanon Ta Kai Karar Isra'ila Ga Babban Sakataren MDD Kan Keta Hurumin Sararin Samaniyarta

18:03 - December 20, 2021
Lambar Labari: 3486708
Tehran (IQNA) Bayan ganawa da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Shugaban Majalisar Dokokin Labanon ya soki gwamnatin sahyoniyawa da keta sararin samaniyar kasar Labanon wajen kai wa Siriya hari.
A wani taron manema labarai na hadin gwiwa tsakanin babban sakataren MDD Antonio Guterres da shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berri a birnin Beirut, Berri ya koka kan yadda gwamnatin Isra'ila ke ci gaba da keta hurumin sararin samaniyar kasar Lebanon.
 
Da yake yabawa da taimakon da Majalisar Dinkin Duniya ke baiwa sojojin kasar Lebanon wajen kare kan iyakar kasar, Nabih Berri ya ce: "Muna yabawa da kokarin mutanenmu a kudancin Lebanon tare da sojoji da kuma dakarun UNIFEL.
 
Shugaban majalisar dokokin kasar Labanon ya bayyana cewa a kullum Isra'ila na keta hurumin sararin samaniyar yankin kasar Labanon, kuma a wasu lokuta suna amfani da yankin mu wajen kai wa kasar Siriya hari.
 
Berry ya ce "Muna son a gudanar da tattaunawa a karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya tare da halartar Amurkawa, saboda jinkirin shawarwarin yana shafar tattalin arzikinmu da kuma jinkirta magance rikice-rikice."
 
A nasa bangaren babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa, Berry ya sanar da mu halin da ake ciki na keta haddin sararin samaniyar kasar Labanon, kuma mun yi la'akari da batun karin taimakon da kasashen duniya suke baiwa sojojin kasar Lebanon, sannan kuma za a duba batun matsalar iyakokin teku tsakanin Lebanon da Isra'ila, domin ita ma Lebanon ta samu damar amfana da albarkatunta na cikin ruwa.
 
 
captcha