IQNA

Ana zanga-zanga a Moroko a ranar tunawa da cika shekara da kulla alaka yahudawan sahyoniya

22:40 - December 23, 2021
Lambar Labari: 3486720
Tehran (IQNA) Mutanen kasar Moroko sun gudanar da zanga-zanga a birane daban-daban domin tunawa da zagayowar shekara guda da kulla alaka da gwamnatin sahyoniyawa.

Tashar France 24 ta bayar da rahoton cewa, Masu zanga-zangar dai sun yi ta rera taken nuna adawa da sasantawa da gwamnatin sahyoniyawan da kuma yin kira zuwa ga soke yarjejeniyar sulhu da suka kira "yarjejeniya mai muni da cin amana."

A cewar wasu majiyoyin, magoya bayan Falasdinawa sun fito kan tituna bisa gayyatar da kungiyoyi daban-daban a kasar ta Moroco, domin bayyana matsayar al'ummar kasar kan matakin da gwamnatin kasar ta dauka na kulla alaka da gwamnatin yahudawa.
 
Ministocin harkokin wajen Morocco da Isra'ila da Amurka sun halarci wani taron bidiyo na tunawa da ranar da aka daidaita alaka tsakanin Isra'ila da Maroko.
 
"Rabat ta kuduri aniyar taimakawa wajen samar da dawwamammen zaman lafiya a yankin," in ji ministan harkokin wajen Moroko a taron na bidiyo.
 
Dangane da rikicin Falasdinu kuwa, ya jaddada goyon bayan kasar Maroko wajen samar da kasashe biyu.
 
Ministan harkokin wajen Moroko ya kuma amince da gayyatar da Lapid ya yi masa na ziyartar yankunan Falastinawa da Isra'ila ta mamaye.
 
A ranar 22 ga watan Disamba, 2020, a karkashin jagorancin gwamnatin Amurka a lokacin shugabancin  tsohon shugaban kasar, Donald Trump, Morocco ta rattaba hannu kan yarjejeniyar maido da huldar jakadanci da gwamnatin sahyoniyawan.
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4023001
 
 
 
captcha