IQNA

Firayi Ministan Pakistan Ya Jinjina Wa Putin Kan Kare Matsayin Manzon Allah (SAW) Da Ya Yi

22:04 - December 26, 2021
Lambar Labari: 3486732
Tehran (IQNA) firayi ministan kasar Pakistan ya jinjina wa shugaban kasar Rasha kan kare matsayin ma'aiki (SAW) da ya yi.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, firayi ministan kasar Pakistan Imran Khan ya fitar da sako a cikin shafinsa na twitter da ke jinjina wa shugaban kasar Rasha  Vladimir Putin, kan kare matsayin ma'aiki (SAW) da ya yi, inda ya bayyana cewa babu yadda za a yi cin mutuncin manzon Allah Muhamamd (SAW) ya zama 'yancin fadar albarkacin baki ko bayyana ra'ayi.

Firayi ministan na Pakistan ya ce yana da kyau musulmi su watsa wannan sako na shugaban Rasha domin al'ummomin duniya su san cewa cin zarafin manzon Allah ba 'yancin fadar albarkacin baki ba ne, batunci ne ga al'ummar musulmi baki daya.

A taron manema labarai da ya saba gabatarwa kafin ranar kirsimatia  kowace shekara, shugaba Vladimir Putin na Rasha ya jaddada cewa, babu yadda za a yi keta alfarmar  wani abu mai tsarki a wajen wasu mutane ko abin da suke girmamawa, hakan ya zamanto cikin 'yancin fadar albarkacin baki ko bayyana ra'ayi.

Ya kara da cewa: Irin wadannan ayyuka na iya haifar da karin kiyayya da tsattsauran ra'ayi a duniya.

 

4023461

 

captcha