IQNA

Shugaban Venezuela Ya jinjina Wa Janar Qassem Sulaimani

15:25 - December 28, 2021
Lambar Labari: 3486741
Tehran (IQNA) shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya jinjina wa Shahid Qasem Sulaimani da jagoran juyi na Iran.

A wata hira da gidan Talabijin din Al’mayadeen na kasar Labanon yayi da shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya fadi cewa ya kamata hukumomi masu fada aji na duniya da sun yi tir da kisan da aka yi wa babban kwamandan yaki da ta’addanci na kasar Iran kasim Sulaimani wanda yayi shahada sakamakon hari da jirgi mara matuki da Amurka ta kai masa a watan janerun shekarar da ta gabata.

Ya ci gaba da cewa Iran tana da kyakkawar dagantaka da sauran kasashen kudancin Amurka ,kuma da sannu zai kawo ziyara Iran , kuma kasarsa ta amince da sabbin yarjeniyoyin da aka kulla tsakaninsu da sabuwar gwammnatin Ibrahim Ra’isi

Haka zalika a tattaunawar ta su shugaban na Venezuel ya fadi cewa ya jinjina wa jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Ayatullah Khaminae kuma ya bayyana shi a matsayin mutum mai hikima da zurfin tunani,

A gefe guda kuma da ya fadi cewa kasar sa ba za ta taba yin watsi da Alummar falasdinu ba, kuma ya yi kira ga hukumomi masu fada aji na duniya musamman majalisar dinkin duniya da su taka muhimmiyar rawa wajen ganin an kwatowa falasdinawa hakkokinsu da Isra’ila take takewa da goyon bayan Amurka.

captcha