IQNA

Kungiyoyin Falastinawa Sun Mayar Da Martani Kan Ganawar Mahmud Abbas Da Ministan Yakin Isra'ila

16:46 - December 30, 2021
Lambar Labari: 3486757
Tehran (IQNA) kungiyoyin Falastinawa suna ci gaba da mayar da martani dangane da ganawar da shugaban Falastinawa Mahmud Abbas ya yi da miistan yakin Isra'ila.

Kakakin kungiyar gwagwarmaya ta Hamas Hazem Qasim ta yi fatali da ganawar da ta gudana tsakanin shugaban gwamnatin kwarya kwaryan cin gashin kai ta Falasdinu Mahmud Abbas Abu Mazin da kuma ministan yaki na Isra’ila Benny Gantz, kana ya bayyana matakin zai kara zurfafa sabanin dake tsakanin bangarorin siyar falasdinu, da kuma kara dagula al’amura. Kuma matakin dawo da hulda da Isra’ila da wasu kasashen larabawa suka yi yana raunan matsayin falasdinu.

Ganawar da Mahmud Abbas ya yi da ministan yaki na Isra’ila yana zuwa ne adaidai lokacin sojojin Isra’ila suke ci gaba da farma masu zanga-zangar ci gaba da gine gine matsugunnan yahudawa a yankunan falasdinawa da ta mamaye a gabar yammacin kogin Jodan dama wasu sassa daban daban.

Mahamud Abbas ya ziyarci gidan wani babban jami’in Isra’ila a karon farko a cikin shekara 10, kuma bangarorin biyu sun tattaunawa kan muhimman batutuwa da suka shafi tsaro a ganawar tasu ta tsawon sa'a biyu da rabi, kuma wannan itace ganawa ta 2 da bangarori suka yi tun bayan kafa sabuwar gwamnatin Isra’ila.

 

 

4024640

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kungiyoyi falastinawa shugaban hamas
captcha