IQNA

Sakamakon Bincike: An samu Karuwar Kyamar Musulunci A Turai A 2020

21:44 - December 30, 2021
Lambar Labari: 3486758
Tehran (IQNA) Wani rahoto na shekara-shekara da aka fitar jiya ya nuna cewa kiyayya da musulunci ta karu sosai a shekarar 2020 a kasashen Turai idan aka kwatanta da shekarun baya.

Rahoton na shekara-shekara da aka fitar jiya Laraba ya bayyana cewa, al'amarin kyamar addinin Islama ya tsananta a nahiyar Turai, kuma shekarar 2020 lamarin ya kara ta’azzara.

"Idan muka yi waiwaye a shekaru shida da suka gabata, za mu ga cewa, masu lura da al'amura da dama sun amince baki daya cewa halin kyamar addinin Islama a Turai bai inganta ba, sai dai ya kara tsananta," in ji rahoton mai shafuka 886 mai taken "Rahoton Turai kan kyamar Musulunci 2020".

Mawallafin rahoton, Anas Birghli, malami a fannin hulda ta kasa da kasa a jami'ar Jamus da ke Istanbul, da kuma Farid Hafez, masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Georgetown da ke Washington DC a Amurka, sun rubuta cewa kyamar Musulunci na daya daga cikin dalilan da suka sanya suka zabi sunan shugaban Faransa Emmanuel Macron,a  matsayin fitacciyar fuskar kyamar muslunci a shekarar 2020.

An gudanar da taron tattaunawa ta yanar gizo mai taken "Kiyayyar Musulunci da Hare-Hare kan 'Yancin Jama'a a Turai" a daidai lokacin da ake gabatar da rahoton na shekara, wanda ake bugawa akai-akai tun shekara ta 2015.

Marubutan wannan rahoto sun ce: "Wannan kuma wata hujja ce a fili cewa yanayin kyamar addinin Islama ya fi tsananta a kasar Faransa da Austria, inda aka rika cin zarafin addinin muslunci a hukuamnce da sunan aiki da dokar yaki da ta’addanci.

Sun kara da cewa rufe kungiyar da ake kira Society Against Islamophobia in France (CCIF) da ke adawa da nuna kyama ga musulmi da nuna musu wariya a kasar Faransa, wani kyakkyawan misali ne na yadda lamarin kyamar Musulunci ke kara yaduwa.

 

4024711

 

 

captcha