IQNA

Kokarin Kasim Sulaimani Da Abu Mahdi Ne Ya Raunana 'Yan Ta'adda A Iraki

22:52 - December 30, 2021
Lambar Labari: 3486760
Tehran (IQNA) Kwamandan dakarun sa kai na larabawan Kirkuk ya ce Kasim Sulaimani da Abu mahdi sun bayar da gudunmawa wajen kubutar da Iraki.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Hatem al-Assi, kwamandan dakarun Larabawa a Kirkuk, ya yaba da sadaukarwar da Janar Qassem Soleimani da Abu Mahdi al-Mohandes, jagororin gwagwarmaya suka yi, ya kuma jaddada cewa idan da ba mu sadaukar da wadannan kwamandojin shahidan ba, yankunanmu za su ci gaba da kasancewa karkashin mamayar Daesh.

“A jajibirin zagayowar ranar shahadar kwamandojin gwagwarmaya, muna tunawa da yadda shugabannin da suka yi nasara suka taka rawa wajen kwato yankunanmu na Hawija, al-Rashad da Riyadh daga hannun kungiyoyin ta’addanci na ISIS tare da kula da ‘yan gudun hijira a yankin da ake yaki, ta hanayar ayyukan jin kai," in ji al-Assi a cikin wata sanarwa.

Ya ce ko shakka babu wadannan manyan kwamandoji sun bayar da babbar gudunmawa wajen kubutar da Iraki daga fadawa hannun 'yan ta'addan Daesh.

Kamar yadda kuma su ne suka kafa dakarun sa kai na Hshd Alshaabi, wadanda har yanzu su ne gishikin zaman lafya a Iraki da kuma hana 'yan ta'adda sakata  fadin kasar.

4024712

 

captcha