IQNA

Shugaba Ra'isi Ya Mika Sakon Taya Murnar Shiga Sabuwar Shekara

23:01 - January 01, 2022
Lambar Labari: 3486767
Tehran (IQNA) A cikin sakonni daban-daban ga shugabannin kasashen Kirista, shugaban Iran Ibrahim Ra’isi ya taya su murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa Almasihu (AS) da kuma shiga sabuwar shekara.

A sakon nasa Ibrahim Ra’isi, ya bayyana cewa: “Abubuwan da ke faruwa a duniya musamman yaki da annobar COVID-19, sun nuna cewa tsaro da makoma na ’yan Adam sun dogara da juna”.
 
Ina taya murnar zagayowar ranar haihuwar Annabin Allah Isa Almasihu (AS) da kuma taya murnar shiga sabuwar shekara ta 2022 miladiyya.
 
Maulidin Annabi Isa Ruhollah (AS) abin kauna ne da farin ciki ga al'ummar Iran; Kuma darajar da Allah ya baiwa annabi Isa abu ne sananne a wurin musulmi, domin kuwa yana daga cikin manyan annabawa manzanni na Allah wadanda dukkanin musulmi suke girmama su, kuma imani da su sharadi daga cikin sharuddan musulunci.
 
Ya ci gaba dacewa, ci gaban duniya, musamman yaƙi da cutar ta Covid, ya nuna cewa tsaro da makomar ɗan adam sun dogara da juna. Hadin gwiwar kasashen da ke cikin wannan matsala musamman a fannin ayyukan samarwa da kuma yin alluran rigakafi, da sauran muhimman abubuwa a fannin kiwon lafiya, ya nuna cewa dole ne a yi aiki tare.
 
Ya ce: ina fatan a cikin sabuwar shekara ta hanyar dogaro da kyawawan halaye na addinan annabin Ibrahim da kuma kokarin hadin gwiwa na gwamnatoci, wahalhalu za su gushe a duniya, kwanciyar hankali da tsayin daka na al'ummomi za su yi amfani, kamar yadda busharar dawowar almasihu take a matsayin wata fata da ke raya ruhi da tunain sake dawowar adalci da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin duniya, ta hanyar isar da sakon Allah madaukakin sarki a gare su.
 
 

4025005

 

captcha