IQNA

A Masar Za A Takaita Karatun Kur'ani A Tarukan Kasa Ga Mambobin Kungiyar Makaranta Ta Kasa Kawai

21:45 - January 02, 2022
Lambar Labari: 3486772
Tehran (IQNA) Kungiyar masu karatun kur'ani mai tsarki a kasar Masar ta sanar da cewa, tana da niyyar zartar da dokar takaita karatun kur'ani da zaman makoki a kasar ga mambobin kungiyar masu karatun kur'ani mai tsarki kawai.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Kungiyar masu karatun kur’ani mai tsarki a kasar Masar ta sanar da cewa ta yi gyara ga wasu daga cikin dokokin kungiyar domin shirya karatun kur’ani  ga wadanda ba mamba ba.

Shugaban kungiyar masu karatun kur’ani mai tsarki a kasar Masar Sheikh Mohammad Saleh Heshad ya bayyana cewa, dokar kungiyar ba ta tabbatar da cewa ko lamarin zai shafi gasar karatun kur’ani mai tsarki ba.
 
A baya kungiyar masu karatun kur’ani mai tsarki ta Masar ta sanar da cewa an kafa wani kwamiti da zai kammala gyaran dokar ta musamman ta kungiyar tare da gabatar da ita  ga ministan ma'aikatar kula da harkokin addini.
 
kungiyar masu karatun kur’ani mai tsarki ta kasar Masar ta sanar a ‘yan watannin da suka gabata korar Hani Saad Mahmoud Abdelhab, dan majalisar gudanarwar kungiyar, tare da cire sunansa daga cikin jerin masu karatu na kungiyar, a cewar wani rahoto da kwamitin tantance na kungiyar ya fitar.
 
Haka nan Sheikh Al-Azhar ya kore shi daga limancin masallacin cibiyar Azhar.
 

4025348

 

 

 

captcha