IQNA

Al'ummar Iraki Na Kan Bakansu Na Neman Ganin Amurka Ta Fice Daga Kasarsu

20:27 - January 03, 2022
Lambar Labari: 3486775
Tehran (IQNA) Kakakin kungiyar Nujba a kasar Iraki ya sanar da cewa, babu gudu babu ja baya wajen aiwatar da shirin fitar da Amurka daga kasar Iraki.

Kakakin kungiyar Nujba Nasr Al-shummari ne ya bayyana hakan a zantawarsa da jaridar Alwifaq, inda ya bayyana cewa, fitar da sojojin Amurka daga kasar Iraki kudiri ne na al’ummar kasar, domin majalisar dokokin kasar ce ta fitar da wannan kudiri, a kan haka ya zama dole a aiwatar da shi.

Ya ci gaba da cewa, Amurka ce ummul haba’isin dukkanin matsalolin tsaro da kasar Iraki ke fama da su, da hakan ya hada har da matsalar ayyukan ta’addancin kungiyoyi irin su Daesh, wadanda ya ce akwai kwararan dalilai da ke tabbatar da alaka da ke tsakanin wadannan kungiyoyi da Amurka.

A kan haka ya ce, ficewar sojojin Amurka daga Iraki za ta kasance ta hanya daya daga cikin hanyoyi biyu, ko dai ta hayar lumana, wato aiwatar da kudirin majalisar dokokin kasar Iraki kamar yadda ya tanadi hakan, ko kuma ficewa babu shiri.

4025678

 

 

 

 

 

captcha