IQNA

Sayyid Nasrallah: Dole Ne Kasashen Yankin Su Bayyana Matsayinsu Kan Kisan Qassem Sulaimani Da Muhandis

18:15 - January 04, 2022
Lambar Labari: 3486778
Tehran (IQNA) Sayyid Nasrulla ya ce dole kasashen yankin gabas ta tsakiya su bayyana matsayinsu kan kisan Kasim Sulaimani da Abu Mahdi Muhandis da Amurka ta yi.

Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon ya ce babban kwamandan yaki da ta'addanci na Iran Laftanar Janar Qassem Soleimani, wanda aka kashe a wani harin da jiragen yakin Amurka suka kai a kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na Bagadaza, ya yi tsayin daka a Iraki da makwabciyarta Syria domin nuna adawa da kasancewar sojojin mamaya na Amurka.
 
Sayyed Hassan Nasrallah ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a gidan talabijin a yammacin jiya Litinin, yayin da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru biyu da kisan gillar da aka yi wa Janar Soleimani, kwamandan dakarun Quds na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) a birnin Beirut.
 
Janar Qassem Solaimani, da Abu Mahdi al-Muhandis tare da wasu dake tare da su sun yi shahada ne a wani harin da jiragen yakin Amurka suka kai wanda tsohon shugaban kasar Donald Trump ya ba da izini a kusa da filin jirgin sama na Bagadaza a ranar 3 ga Janairu, 2020.
 
"Kasancewar sojojin Amurka a yankin bai haifar da komai ba illa barna, zubar da jini da hadassa gudun jihira," in ji Hassan Nasrallah, yana mai cewa kisan gillar da aka yi wa manyan kwamandojin yaki da ta'addanci guda biyu yana da matukar tasiri ga daukacin yankin gabas ta tsakiya.
 
Ya kara da cewa, Janar Soleimani da Muhandis sun yi fice a duk fadin yankin, inda ya kara da cewa kowa na iya daukar darasi daga shahadarsu.
 
 

 

 

captcha