Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, Ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta sanar da gudanar da gasar tantance makaranta da za a tura su karatun kur'ani mai tsarki zuwa kasashen waje a cikin watan Ramadan mai zuwa.
Za a gudanar da wannan gasa ne a tsakanin fitattun malamai daga cikin limamai da masu shirya tarurrukan addini da ma'aikatan cibiyoyin addini da kuma ma'abota karatu na kungiyar masu karatu da kuma fitattun masu karantu a gidajen rediyo da talabijin.
Masu neman shiga gasar dole ne su cika wasu sharudda, kamar gabatar da takardun shedar zama memba a ƙungiyar masu karatu, ko gabatar da karatu a rediyo da talabijin, cin jarrabawar rubuce-rubuce, da kuma shaidar da ke tabbatar da mutum bai taba aikata wani mummunan laifi ba.
Ana gudanar da jarrabawar share fage ne a ofisoshi na yankuna, sannan kuma a gudanar da jarrabawar karshe a ofifin babban daraktan ma’aikatar kula da addini.
https://iqna.ir/fa/news/4026625