IQNA

Ana Neman tallafa wa yarinya mai larura kuma mahardaciyar kur'ani a Syria

22:52 - January 08, 2022
Lambar Labari: 3486795
Tehran (IQNA) Wata yarinya ‘yar shekara biyar ‘yar kasar Syria, duk da cewa tana fama da ciwon Autism, tana da ilimi da hazaka sosai.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, Wata yarinya ‘yar shekara biyar ‘yar kasar Syria, duk da cewa tana fama da ciwon Autism, tana da ilimi da hazaka sosai, kuma ta iya haddace kur’ani mai tsarki gaba daya, kuma tana iya magana da rayayyun harsuna da dama na duniya.

Sari Azzam yarinya ce ‘yar shekara biyar ‘yar kasar Syria wacce aka gano tana da nau’in cutar Autism tun tana shekara biyu, sai dai masana a kasar sun ce baiwa ce irin tata.

Sari, wadda ta iya ɗaukar alƙalami da kuma gwada rubuta kalmomi tun tana shekara biyu, yanzu tana ɗaukar sa'o'i a kowace rana tana koyon Turanci, Faransanci, Koriya, Jafananci, Girkanci, Sipaanci da wasu harsuna da dama a kan layukan yanar gizo tana da shekara biyar. 

Mahaifiyar Sari tana fatan yarinyarta za ta sami kulawa mai zurfi wanda ya dace da bukatunta kuma tana so hakan ya taimaka mata wajen lamrinta na addini.

4027098

 

captcha