Shafin Al-shuruq ya bayar da rahoton cewa, Wannan littafi ya ba da dogon bayani kan tarihin makarantar kur’ani ta Masar tun daga farkon karni na ashirin.
Marubucin littafin ya ce: wannan littafi ya hada abubuwa masu tarin yawa da suke da alaka tsakanin ilmomin wadannan manyan malaman kur'ani na kasar Masar.
A cikin wannan littafi, an gabatar da manyan masu karanta tarihin Masar daga wani nau'i na daban kuma na musamman, kuma dangantakarsu da yadda makaranta suke amfani da salo na musamman wajen kyautata karatun kur'ani.
An zabo rukunoni bakwai na makarantar kur’ani ta Masar a cikin wannan littafi, da suka hada da Muhammad Rafat, Mustafa Ismail, Abd al-Basit, Manshawi, al-Banna, al-Husari, da Tablawi.