Kungiyar Dastak ta kasar Turkiyya dake gudanar da ayyukanta a zirin Gaza ta gabatar da mujalladi 20,000 na kur'ani mai tsarki ga ma'aikatar wakafi da harkokin addini a Gaza a ranar Lahadin da ta gabata don rabawa a masallatai da cibiyoyin koyar da haddar kur'ani.
Hani Suray, shugaban kungiyar Ghazi Dastak, ya ce rabon wadannan kwafin wani bangare ne na isar da sakon "Al-Qur'ani, wanda aka gudanar a karkashin kulawar wata cibiyar kula da harkokin addini ta Turkiyya.
Ya kara da cewa: Kimanin mujalladi 50,000 na kur'ani ne za a raba a kasar Falasdinu a wani bangare na wannan aiki, inda za a raba mujalladi 20,000 ga Gaza da mujalladi 30,000 ga yammacin gabar kogin Jordan, ciki har da birnin Kudus.
Surayya ya jaddada cewa, za a raba kwafin kur'ani mai tsarki da aka kaiwa ma'aikatar kula da addini ta Gaza a masallatai da da'irorin haddar kur'ani.