IQNA

An Kori limamin wani masallaci a Belgium bisa zargin yin barazana ga tsaron kasar

22:52 - January 14, 2022
Lambar Labari: 3486819
Tehran (IQNA) Gwamnatin Belgium ta kori limamin wani masallaci a Brussels babban birnin kasar, bisa zargin yin barazana ga tsaron kasar.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Minista mai kula da 'yan gudun hijira da shige da fice na kasar Belgium, ya hana limamin masallacin Hebron da ke gundumar Moulinbeek da ke birnin Brussels zama a kasar bisa zarginsa da yin barazana ga tsaron kasar.

A cewar shafin yanar gizo na VRT News, matakin ya samo asali ne daga wasu bayanai daga jami'an tsaro, inda suka yi ikirarin cewa Limamin dan asalin kasar Moroko babban barazana ce ga tsaron kasar.

An soke izinin zaman Sheikh Tijani kuma an kore shi, duk da cewa an san shi a matsayin daya daga cikin manyan masu wa'azin musulmi a Belgium.

Da yake tabbatar da labarin soke izinin zaman nana, Ministan na Belgium ya ki bayar da karin bayani kan yanayin barazanar, yana mai cewa: “Wannan mataki sako ne ga masu saka kiyayya, da raba kan al’umma da barazana ga tsaron kasa, da makamantansu, wadanda ya ce Belgium ba ta maraba da su.

 

4028430

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: maraba
captcha