IQNA

Tsohon Limamin Masallacin Haramin Makka Ya Sake Bayyana A Cikin Wani Fim Na Talla

16:37 - January 17, 2022
Lambar Labari: 3486832
Tehran (IQNA) tsohon limamin masallacin haramin Makka Adel kalbaniya sake bayyana a cikin wani fim na talla.

Tashar CNN Arabic ta bayar da rahoton cewa, Adel Kalbani wanda ya shahara a matsayin daya daga cikin manyan malaman gwamnatin Saudiyya, kuma tsohon limamin haramin Makka, ya sake bayyana a cikin wani fim na talla.Wannan lamari dai ya dauke hankula matuka a shafukan yanar gizo a kasar ta Saudiyya da kuma wasu daga cikin kasashen larabawa, inda da dama suke bayyana ra’ayinsu dangane da hakan, tare da bayyana cewa bai dace da matsayi na mutum da ya shahara a matsayin malamin addini ba.

Ko a kwanakin baya Adel Kalbani ya bayyana a cikin wani tallar wani fim, wanda shi ma ya fuskanci kakausan martani daga bangarori daban-daban na larabawa da musulmi a sassa na duniya.

Malamin dai yana kokarin aiwatar da sabuwar siyasar yarima mai jiran gadon kasar ta Saudiyya ne, da ke son mayar da kasar kamar sauran takwarorinta na larabawa, ta hanayar kirkiro sabbin abubuwa da a lokutan baya malaman kasar suke haramtawa suke kiran hakan bidi’a ko shirka.

Idan za a iya tunawa shekaru biyu da suka gabata, an bude gidan karta a birnin Riyadh, inda Adel kalbani ya kaance daya daga cikin wadanda suka halarci bikin buden gidan kartar, har ma aka nuna hotunansa yana lale karta a hannunsa da kuma rabawa ga wasu mutane da suke zaune a kan wani tebur a wurin, lamarin da shi ma ya fuskanci kakkausar suka.

4029063

 

 

captcha