IQNA

Kwafin Alqur'ani 21,000; Gudunmawar shekara guda da Turkiyya ta baiwa Afirka

22:43 - January 17, 2022
Lambar Labari: 3486834
Tehran (IQNA) Wata kungiyar ba da agaji a kasar Turkiyya ta sanar da cewa a shekarar 2021 ta baiwa daliban haddar kur'ani mai tsarki a kasashe 7 na Afirka gudummawar kusan kwafin kur'ani mai tsarki 21,000.

Kamfanin dillancin labaran Turkiya ya bayar da rahoton cewa, kungiyar Bayar da Agaji ta Turkiyya (IHH) a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, da yawa daga cikin yara da matasa musulmi a duniya na haddace kur'ani mai tsarki ta hanyar amfani da allunan gargajiya.

Kungiyar ta ce a bara, an raba kwafin kur’ani 13,500 ga daliban kasashen Guinea da Mali, da na Chadi guda 2,900, ga daliban kasar Chadi 2,000, a Ghana, 2,000 a Nijar da Sudan, da kuma 600 a Saliyo.

Kungiyar ta kara da cewa kawo ya zuwa yanzu ta raba kwafin  kur'ani mai tsarki 263,000 ga mabukata a kasashe daban-daban.

 

4029183

 

 

 

captcha