IQNA

Paparoma Ya Bukaci Yin Addu'a Domin Samun Zaman Lafiya A Duniya

15:17 - January 26, 2022
Lambar Labari: 3486869
Tehran (IQNA) Paparoma Francis, na fadar Vatican, ya ba da shawarar cewa a yau Laraba 26 ga watan Fabrairu kowa ya yi addu’ar samun zaman lafiya.

Paparoma Francis ya ce, "Na damu matuka game da karuwar tashe-tashen hankula, wanda ya haifar da wani sabon koma baya ga zaman lafiya a Ukraine da kuma tsaron nahiyar Turai," in ji Paparoma Francis, yayin da yake magana kan rantsar da wasu limaman Kirista guda biyu,

Ya ci gaba da cewa: “Ina rokon jama’a a duniya da su yi addu’a ga Allah domin ayyukan siyasa su zama na ‘yan’uwantaka da mutuntaka ba muradun kashin kai da na daidaiku ba, domin samun zaman lafiyar dukkanin al’ummomi.

 Paparoma ya kara da cewa: “Dukkanmu ‘yan’uwa ne, don haka tare da nuna damuwa tare da la’akari da halin da ake ciki yanzu, ina ba da shawarar cewa a yau Laraba 26 ga watan Janairu ta kasance ranar addu’ar neman zaman lafiya.

Yankin Donbas yana gabashin Ukraine ne wanda mazaunansa Rashawa ne, kuma tun daga shekara ta 2014, Rashawan wannan yanki suka kafa jamhuriyoyin Donetsk da Lugansk guda biyu masu cin gashin kansu, kuma sun kafa kananan hukumomi masu cin gashin kansu a cikin kasar ta Ukraine.

Rasha ta sha yin kira ga gwamnatin Ukraine da ta tattauna da wakilan yankunan biyu domin cimma matsaya da warware takaddama, amma Kiev ta ki goyon bayan Moscow kan hakan, a maimakon hakan ma tana zargin Rasha ne da marawa Rashawan yankunan gabshin Ukraine baya.

4031568

 

captcha