IQNA

Kungiyar malaman musulmi ta kasar Lebanon ta yi Allah wadai da kalaman Charles Jabour

23:21 - January 31, 2022
Lambar Labari: 3486891
Tehran (IQNA) Kungiyar malaman musulmi ta kasar Labanon ta yi Allah wadai da kalaman da babban jami'in yada labarai na kungiyar Lebanese Forces da ya yi game da kungiyar Hizbullah inda ta bayyana hakan a matsayin cin mutunci ga Musulunci.

Shafin yada labarai na al'ahad ya bayar da rahoton cewa, Kungiyar malaman musulmi ta kasar Labanon ta yi Allah wadai da kalaman da babban jami’in yada labarai na kungiyar Lebanese Forces ta Samir Jaja,  inda ta bayyana hakan a matsayin cin mutunci ga addinin Musulunci.

A nasa jawabin, Jabour ya kira akidar Hizbullah a matsayin wauta da ke da alaka da zamanin dutse yana mai ishara da zamanin bayyanar addinin muslunci.

Kungiyar malaman musulmi ta kasar Lebanon ta yi kira ga gwamnatin kasar Lebanon da ta gurfanar da Charles Jabour a gaban kuliya domin hukunta shi kan kalaman da ya yi.

Da wadannan kalamai ne Jabor ya nemi ya kunna wutar bangaranci a kasar Labanon, duk da cewa mutanen kasar masu ilimi ba za su bari ya yi hakan ba a cewar kungiyar malaman addini ta kasar Lebanon.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta yi kira ga Darul Fatawa, Majalisar Koli ta mabiya Shi'a, da Majalisar Dattawan kabilar Druze da su gurfanar da shi a gaban kuliya bisa laifin da ya aikata na wulakanta addinin musulunci.

Kungiyar Lebanese Forces dai kungiya ce ta kiristoci a Lebanon wadda take yi wa Isra'ila aiki a cikin kasar, inda ta kasance a  sahun gaba wajen taimaka ma Isra'ila a lokacin da ta mamaye wasu yankunan kasar Lebanon.

A halin yanzu kasashen Saudiyya da Amurka ne suke daukar nauyin ayyukan kungiyar a  kasar Lebanon.

 

4032832

 

captcha