IQNA

Da'irorin kur'ani a kudancin Labanon a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar lokacin aiko ma'aiki (SAW)

14:53 - February 25, 2022
Lambar Labari: 3486980
Tehran (IQNA) Kungiyar al'adun muslunci ta kasar Labanon "Maaref" tana gudanar da tarukan kur'ani a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan ranar 27 ga watan Rajab.

A ranar Lahadi mai zuwa ne za a fara gudanar da da'irar kur'ani mai tsarki har zuwa ranar 4 ga Maris na wannan shekara.
Wadannan da'irar Al-Qur'ani na Maulidin Manzon Allah (s.a.w) a Masallacin Imam Ali (AS) da ke garin "Al-Hawsh" masallacin Imam Husaini (AS) da ke garin "Deir Qanun Ras Al-Ain" da Masallacin Imam Ali (AS) da ke " Garin Al-Bazouria, Masallacin garin "Maskaba", Masallacin "Al-Madrasa Al-Diniya" a cikin birnin "Tire" dake kudancin kasar Lebanon.
Ana watsa shirye-shiryen wadannan da'irorin Alkur'ani kai tsaye a Facebook.
Aiko ma’aiki Annabi Muhammad (SAW) a matsayin Annabi da kuma farkon manzancinsa, wanda a cewar mashahuran ruwayoyi  ya faru ne a ranar 27 ga watan Rajab shekara ta arba’in ta giwaye.
Don haka a ranar 27 ga Rajab na a matsayin ranar aiko Manzon Allah (SAW) shi ne farkon addinin Musulunci da share fage na kawar da bautar gumaka daga Hijaz.
 
https://iqna.ir/fa/news/4038595

Abubuwan Da Ya Shafa: rajab
captcha