IQNA

Rahoton MDD: yara kimanin 10,000 aka kashe a yakin Yemen

17:29 - March 17, 2022
Lambar Labari: 3487064
Tehran (IQNA) rahoton majalisar dinkin duniya ya ce daga lokacin da Saudiyya ta fara kai hari kan al’ummar Yemen ya zuwa yara kimanin 10,000 ne suka mutu sakamakon hare-haren.

Da yake sanar da hakan yayin wani taro ta kafar bidiyo na samar da tallafi ga kasar ta Yemen, Mista Guteress, ya ce gwamman dubban fararen hula ne yakin na Yemen ya rusa dasu ciki har da yara kimanin 10,000.

Haka zalika kuma yakin ya tilastawa wasu milyoyin ‘yan Yemen din yin hijira.

Ya kara da cewa an daina maganar yakin na Yemen, amma har yanzu jama’ar kasar na cikin ukuba, kuma rashin kudade zai kara jefa kasar cikin ba’la’I, baya ga matsananciyar yunwa da milyoyin jama’ar kasar ke fama da ita a cewar Babban sakataren na MDD.

Hakan kuma ya sanya hukumar kula da abinci ta MDD ta rage yawan abincin da take bayarwa saboda karancin da takle fama da shi.

Idan kuma ba’a dauki matakin gaggawa ba, sama da mutum miliyan hudu zasu rasa hatta ruwan sha sabtattace a kasar Yemen inji MDD.

 

https://iqna.ir/fa/news/4043732

captcha