Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazeera cewa, mazauna kauyukan yankin Urmia na kasar Habasha sun shaida bikin yaye dalibai 700 da suka haddace kur’ani mai tsarki daga wata cibiya ta addinin musulunci mai suna Zayd bin Thabet.
Wani mai wa'azin kasar Habasha Sheikh Amin Ebru ya fitar da hotuna da bidiyo na bikin, inda ya nuna masu haddar kur'ani sun yi layi a cikin sahu suna tafiya a kan titunan kauyen domin murnarsu.
Wadannan mutane suna zuwa masallatai daban-daban don gudanar da tarukan ibada na musamman a wannan wata.