IQNA

An karbe Tarin kwafin kur'ani da aka buga da kura-kurai  a Jordan

16:43 - May 19, 2022
Lambar Labari: 3487312
Tehran (IQNA) Ma'aikatar da ke kula da harkokin kyauta ta kasar Jordan ta ba da umarnin karbar kur'ani mai tsarki da aka shigo da su daga kasashen ketare sakamakon matsalar bugu da wasu ayoyin.

A cewar shafin larabci mai lamba 21, ma’aikatar kula da harkokin kyauta ta kasar Jordan a jiya Laraba ta umurci kungiyoyin da ke da alaka da ita da su nemi dukkanin limamai da masu wa’azi maza da mata da masu kula da gidajen kur’ani mai tsarki da su karbi kwafin da wasu cibiyoyi 3 na kasar waje suka buga a kasar, sannan a goge su saboda kurakurai na rubutu.

Abdullah al-Aqeel, babban sakataren ma’aikatar kula da da’a, da harkokin addinin musulunci da kuma wurare masu tsarki na kasar Jordan ne ya bada umarnin ga jami’an. Kamar yadda Al-Aqeel ya ce, a aya ta 67 a cikin suratun Nisa’i da aya ta 1 a cikin suratun Anfal, an yi kuskuren rubutun rubutu kuma an bar wani bangare na surar Shu’ara.

Wani jami'in ma'aikatar ya ce: "Ya zama al'ada a buga odar karbar kwafin kur'ani mai tsarki da wannan ma'aikatar ta fitar, domin wannan hukuma ta kuduri aniyar cewa a bisa doka, babu wani kwafin da zai shigo kasar ba tare da izini ba."

Jami'in ya kara da cewa: An buga kwafin kur'ani mai tsarki da ke kunshe da kura-kurai daga gidajen buga littattafai na kasashen waje kuma an shigo da su kasar Jordan da yawa daga kasashen waje. Haka kuma ma’aikatar ta tuntubi gidajen buga littattafai domin gyara matsalolin da ake da su.

 

Ya ce an tattara wasu daga cikin wadannan kwafin shekaru da suka gabata kuma an sake buga wannan odar don tabbatar da cewa babu kwafin da ya rage.

 

https://iqna.ir/fa/news/4058142

captcha