A jajibirin watan Muharram mai alfarma da kuma ranakun juyayin zagayowar ranar shahadar Aba Abdullah Al-Hussein (a.s) da sahabbansa muminai, da Sayyidina Abbas (a.s) an dora tutocin juyayi da kuma kawata sunaye da lakabin Imam Hussaini da Sayyiduna Abbas (a.s) tare da sanya bakaken kyallaye da kuma a shirye-shiryen tarbar dimbin masu juyayi.