Firayi ministan kasar Iraki Mustafa Alkazimi ya sanar da cewa, an dauki dukkanin matakan da suka dace domin tabbatar da cewa tarukan sun gudana lami lafiya, tare da sanar da cewa ranar Lahadi mai zuwa za ta kasance ranar hutu a hukumance, kasantuwar tarukan na Arbaeen za su kasance ne a ranar Asabar.
Gwamnan Lardin karbala ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu miliyoyin mutane suka iso birnin domin halartar wadannan taruka, kuma an dauki dukkanin matakan da suka dace na daukar bakuncin masu ziyara, da hakan ya hada da daukar kwararan matakan tsaro, samar da ababe bukatar rayuwa, da kuma tanadin kayayyakin ayyuka a bangaren lafiya.
A ranar Asabar mai zuwa ce za a gudanar da tarukan na arbaeen a birnin karbala, wanda ake sa ran mutane fiye da miliyan 20 za su halarta, daga ciki da wajen kasar Iraki.