Bangaren Siyasa:manufar juyin musulunci kin Zalumci da kin aikata shi,a yau jamhuriyar musulunci ta nada alaka ami kyau da sauran al'ummomi da suke a shirye zukatansu suke su hade da juyin musulunci na Iran.
A wani rahoto da cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ta bayyana cewa a lokacin taron baje kolin tunawa da nasarorin juyin musulunci a cikin shekaru talatin da suka gabata a ranar litinin da aka samu halartar sakataren kula da shirye-shirye da sa ido a ofishin shugaban kasa har ila yau shugaban bababr hukumar bincike ta kasa manayn baki sun bayyana irin nasarorin da aka samu a cikin wadannan shekaru talati na juyin musulunci a nan Iran.Ayubi shugaban shirya wannan kasuwar baje koli a lokacin da yak e gabatar da jawabin bude taron baje koli ya yi nuni da ayyukan da banagarori 530 suka yi karkashin wannan kasuwa da cewa; A fadin Iran za a gudanar da irin wannan bincike da baje koli domin al'ummar Iran su shaida a gaban idonsu irin nasarorin da Iran ta samu a cikin shekaru talatin kacal. Kuma ya kara da cewa shugabanni da jagororin al'umma a fadin Iran za su ci gaba da jan aikin da suka dukufa domin cimma wasu nasarorin a nan gaba. Tare da bada misalign da tauraron dan adam mai suna Umid da Iran ta jefa da cewa yana daga cikin kokari da nasarar Imam Khomeini ®.
353476