IQNA

Dan majalisar kasar Holand mai tsananin gaba da addinin Musulunci ya yi kakkausar Kan Ingila mahukuntan kasar Birtaniya, bayan da suka hana shi shiga kasar

14:09 - February 15, 2009
Lambar Labari: 1744499
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kafar yada labarai ta BBC cewa, an hana Geert Wilders shiga cikin kasar Birtaniya bayan da ya isa filin safka da tashin jiragen sama na birnin London, inda ya bayyana hakan da cewa wani babban cin zarafi ne aka yi masa, domin kuwa wasu 'yan majalisar dokokin kasar Birtaniya ne suka gayyace shi zuwa kasar domin ya nuna fim dinsa na (Fitina) wanda a cikinsa ya ci zarafin alkur'ani mai tsarki.
Ya kara da cewa hana shi shiga kasar Birtaniya ya sabawa hankali, kuma hakan hana shi bayyana ra'ayinsa da akidarsa ne, wanda ya ce abin takaici ne.

A bangare guda kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida a kasar Birtaniyaya bayyana cewa, gwamnatin Birtaniya ba ta yarda da duk aikin batunci ga wani addini ba, kuma tana fada da duk tsattsauran ra'ayi da wuce gonad a iri, wanda ka iya jawo rikici a cikin kasarta.

Wasu 'yan majalisar kasar Birtaniya biyu ne suka gayyaci (Geert Wilders) zuwa kasar domin ya zo ya nuna fin dinsa na (Fitina) a kasar, amma wasu da dama daga cikin 'yan majalisar kasar sun nuna rashin amincewarsu da hakan.

Tun kafin lokacin mahukuntan kasar Birtaniya sun sanar da hana Geert Wildwers shiga cikin kasar, amma ya yi kunnen uwar shegu da gargadin na mahukuntan Birtaniya, kuma ya isa filin safka da tashin jiragen sama na Birnin London.

363776
captcha