Cibiyar kula da harkokin alkur'ani ta Iran ikna ta nakalto daga jaridar (Al-sharq) da ake bugawa a kasar saudiyya cewa; sakatarn kungiyar OIC Ihsan Auglo ya fitar da wani bayani a jiya da acikinsa ya yi kakkausar suka kan hare-haren ta'addancin da aka kai masu ziyarar Imam Hussain a Karbala da ke kasar Iraki, inda ya bayyana hakan da cewa aiki ne na ta'addanci da ya yi hannun riga da koyarwa irin ta addinin musulunci, ya kira yi dukkanin musulmi da su yi hattara da makircin makiya musulunci da ke neman bata surar addini.
364383