Bangare kasa da kasa: Wani lauya dan kasar Bogaria mai suna Junior Ganif, ya bayyana cewa kur'ani littafi ne mai a cikin tarihin dan adam, kuma babu wani abu da ke nuna kira zuwa ga ta'addanci a cikinsa.
Cibiyar kula da harkokin alkur'ani ta Ikna, ta nakalto daga jaridar (Al-sharq Al-ausat) cewa; Junior Ganif ya fara karanta alkur'ani, domin tabbatar da gaskiya ko rashin gaskiya dangane da abin da wasu ke rayawa, kan cewa littafin kur'ani yana koyar da ayyukan ta'addanci, amma Junior Ganif sakamakon karanta alkur'ani da ya yi baki dayansa, ya gano cewa babu wani abu na tashin hankali ko kira zuwa ga ta'addanci a cikin kur'ani. Inda ya bayyana cewa fahimtar alkur'ani a matsayin wani littafi mai girma dab a shi da dangantaka da abin da ake jingina masa na karairayi, hakan zai taimaka wajen hadin kan mabiya addinai a kasar Bolgaria.
365247