Bangaren ilimi da Fikira: a jiya ne aka kaddamar da bukin kafa majalisar tuntubar juna tsakanin musulmi da kiristoci a Koweiti tare da halartar said baker Mahri limamin masallacin imam Ali (AS) da kuma Radawi Urdigani shugaban ofishin yada al'adu na Iran a koweiti.
Cibiyar kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ce ta watsa bayan ta nakalto daga ofishin kula da al'adu da yada shi na Iran a kasar ta Koweiti ta watsa rahoton cewa; a lokacin kaddamar da wannan majalisa an samu halartar manyan baki da jami'an gwamnati day an siyasa a wannan kasa ta koweiti bugu da kari an samu halartar manyan malumman addinin musulunci da malumman kiristoci na wannan kasa.A lokacin da wakilan musulmi da na kirista ke bayani sun bayyana gamsuwarsu a fili da kaddamar da wannan majalisar da suka ce za ta taimak wajen magance matsalolin da musulmi day an uwansu kiristoci ke fuskanta da kuma bayana irin kokarin da manyan malummai da jagororin al'umma suke a wannan fage kamar Sheikh Mufid,Ayatullah Sistani da jagoran juyin juya halin musulunci a Iran da sauran maraji'o'i.
365536