IQNA

Za A Gudanar Taron Karawa Juna Ilimi Kan Fannonin Alkur'ani A Kasar Saudiyya

Bangaren kasa da kasa: Ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Saudiyya ta habarta cewa za a gudanar da taron karawa juna ilimi kan fannonin alkur'ani da ci gaban zamani a kasar ta Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-riyad) ta kasar Saudiyya cewa; wannan taron karawa juna ilimi za a gudanar da shi ne a birnin Madina mai alfarma, inda taron zai yi dubi kan fannonin ilimi da alkur'ani ya yi Magana kansu, da kuma yadda za a yi amfani da su a zamanance.Bayanin ya kara da cewa taron zai samu halartar masana kan alkur'ani na kasar Saudiyya da ma wasu kasashen musulmi, kuma tuni aka tanadi dukkanin bayanai kan taron taron da kuma yadda za a gudanar da shi. An shirya shafin Internet (www.Quran.org) wanda zai kunshi dukkanin bayanai da suka shafi wannan taro.

367026