IQNA

Kwaciya da Sa'adar Musulmi A Bangaren Hulda Yana Tattare Da Alkur'ani Da Ahlul Beiti (AS)

9:12 - February 23, 2009
Lambar Labari: 1747560
Bangaren Harkokin Alkur'ani: Shekh Azanshah babban malamin yan shi'a a Tailand ya yi nuni da hadisin Sakalain da cewa: sa'adar musulmi a bangaren hulda yana tattare da alkur'ani mai tsarki da ahlul Beiti (AS).
Bangaren cibiyar kula da harkokin Alkur'ani a Iran Ikna da ke kudu maso gabacin Asiya ya watsa rahoton cewa: Shekh Azanshah malamin shi'a a tailand kuma limamin juma'ar garin Kancanaburi a wannan kasa a sallar juma'ar da ta gabata a hudubar day a gabatar ya kara da cewa: Sa'adar karshe ta musulmi tana tare da Alkur'ani da Ahlul beiti (AS) tare da kafa hujja da hadisin Sakalain da Shi'a da Sunna suka amince da shi.Kuma ya jaddada cewa shiriyar dan adam tana tattare da riko da wadannan abubuwa kamar yadda tabewarsa ke tare da watsi da wadannan abubuwa guda biyu ko barin daya daga cikin biyu dab a su rabuwa a tsawon rayuwa a wannan duniya . A wani bangare kuma ya tabo batun adalcin Allah a matsayin babbar ni'imar Allah ga bayunsa da kuma daidaito a tsakanin bayunsa.

366657

captcha