IQNA

- Iraniyawan Da ke Zaune a kasar Maleishiya Za Su Fara Makokin Tunawa Da Korar Ma'aikin Allah (SWA)

9:11 - February 23, 2009
Lambar Labari: 1747563
Bangaren Siyasa da zamantakewa: Iraniyawan da ke zaune a maleishiya sun fara zaman makokin tunawa da korar ma'aikin Allah (SWA) da kuma na shahadar Hasan Mujtaba (AS) kuma za yi wannan zama a biranai da daman a wannan kasa a ranar Talata mai zuwa.
Cibiyar kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga ofishin kula da al'adu na jamhuriyar musulunci a Iran da ke maleishiya ta watsa rahoton cewa: za a gudanar da wannan zaman makokin juyayin korar ma'aikin Allah (SWA) da kuma na shahadar jikansa imam Hasan Mujtaba (AS).Har ila yau ofishin kula da al'adun Iran a Maleishiya zai gudanar da irin wannan zaman juyayi na shahadar imam Rida (AS) a babban birnin kasar da sauran manyan biranan kasar.

367643

captcha