Bangare na kasa da kasa: Jami'an tsaron kasar saudiyya sun kai farmaki kan musulmi masu gudanar da ziyara a masallacin annabi Muhammad (SAW) da ke birnin Madina, tare da jikkata wasu da dama daga cikinsu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga tashar talabijin ta (RASID) cewa; jami'an tsaron gwamnatin saudiyya a cikin kayan sarki sun killace daruruwan musulmi masu ziyara a masallacin manzon Allah, inda suke gudanar da ayyukan ibada a ranar tunawa da wafatin manzon Allah da (SAW) da Imam Hassan Al-mujtaba (AS) inda suke karanta addu'oi na ziyara, amma jami'an tsaron na saudiyya bas u yi wata-wata ba wajen afkawa kansu da duka mai tsanani, inda suka jikkata da dama daga cikin masu ziyarar, tare da yin awon gaba da wasu daga cikinsu, bisa hujjar cewa jami'an tsaron saudiyya suna hana gudanar da ayyukan shirka ne.
368981