Bangaren kasa da kasa: Kwamitin hadin gwiwa da ke gudanar da tattaunawa kan samar da fahimtar juna tsakanin musulmi da kirista tsakanin jami'ar Al-azhar da kuma fadar Vatican, ya bukaci da caja wasu darussa da ke sukar wasu addinai a makarantu
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Faransa (AFP) cewa; dukkanin bangarorin biyu da suke halartar zaman tattaunawar a birnin Roma na kasar Italiya sun amince kan cewa a yi gyaran fuska ga wasu darussa da ke cikin wasu littafai na darasi, da ke sukar wasu addinai, domin a cewar mahalarta zaman hakan zai taimaka matuka wajen warware matsalar rashin fahimtar juna tsakanin mabiya addinai.
Ya zo a cikin wani bayani da mahalarta taron suka fitar cewa; babban nauyin da ya rataya kan jagorin mabiya addinai shi ne, su ci gaba da wayar da kan mabiyansu dangane da muhimmancin da ke tattare samun fahimtar juna tsakaninsu da sauran mabiya wasu addinan.
369853