Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran cew; a zaman da aka gudanar a birnin Geneva na kasar Szitzerland dangane da kawar da makaman kare dangi a duniya, ministan harkokin wajen kasar Iran Manochehr Mottaki ya bayyana cewa; babban burin Iran shi ne a wayi gari babu sauran makaman kare dangi a duniya, domin a cewarsa babbar barazana ga zaman lafiyar duniya ita makaman kare dangi, wanda kuma madamar wasu kasashe za su ci gaba da mallakar irin wadannan makamai, to kuwa duniya ba ta ga zaman lafiya ba.
Ya ce Iran ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya a duniya, kuma za ta ci gaba da yin riko da abin da ta rattaba hannu kansa.
372096