IQNA

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Halarci Taron Goyon Baya Ga Palastinu

16:22 - March 05, 2009
Lambar Labari: 1752095
Bangaren siyasa: Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya halarci taron nuna goyon baya da majalisar shawara ta Iran ta shirya.
Kamfanin dillancin Ikna ya habarta cewa; jagoran juyin juya halin musuluncin a Iran Ayatollah Ozma Sayyid ali Khamenei ya halarci wurin taron nuna goya baya ga al'ummar Palastinu musamman al'ummar gaza, wanda aka fara gudanarwa a birnin Tehran. Jagoran ya gabatar da jawabin bude taron, tare yin maraba ga dukkanin mahalarta taron da suka fito daga kasashen duniya sama 80, inda ya jinjina musu tare yaba kokarinsu na damuwa da halin da 'yan uwansu suka samu kansu a ciki a Palastinu.
Jagoran ya jaddada muhimmancin da ke tattare da daukar lamarin palastinu ya zama mafi muhimmanci a halin yanzu a cikin dukkanin matsalolin da ke cima duniyar musulunci tuwo a kwarya, domin a cewarsa warware matsalar palastinawa warware babban gae ne na matsalar musulmi.

372516


captcha