IQNA

A Duk Lokacin Da Mata Suka Kara Yawa Wajen Kusanci Da sanin Ahlul Baiti (AS) Al'umma Na Gyaruwa

Bangaren siyasa da zamantakewa: Wutar Fasadi ta mamaye duniya musamman a yammacin Turai amma mata Iraniyawa da albarkacin sani da kusanci da Ahlul Baiti (AS) sun kaucewa fadawa cikin wannan tarko.
Daga birnin Qum ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: hujjatul islama Yusuf Gulami masanin harkokin iyali da ke bada karatu a Hauzar ilimi ta birnin Quma lokacin day a halarci jerin gwano na juyayin tunawa da shahadar Fatima Ma'asuma (S) ya bayyana cewa: Mata day an Mata Iraniyawa karkashin albarkacin bin tafarkin Ahlul Baiti (AS) sun kaucewa fadawa tarkon abin da matan Turai suka fada a ciki da kuma barazanar da sauran yan uwansu ke fuskantar.

383559