IQNA

Ana Watsa Wani Bangare Na Fim Din Maryam Mukaddas A Talbijin Din Zimbabwe

Bangaren fasaha: ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a ketare a birnin Harare ya taimaka wajen watsa fim din Maryam Mukaddas a Talbijin din kasar Zimbabwe.
Bayan ta nakalto daga babban ofishin hulda da jama'a da watsa labarai a hukumar yada al'adun Iran a Ketare ,cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; ofishin hukumar da ke a birnin Harare na kasar Zimbabwe ya taimaka wajen watsa fim Maryam Mukaddas (k) a gidan talbijin na gwamnatin wannan kasa. Kuma wannan it ace fim ta Iraniyawa da aka watsa a ketare a wannan sabuwar shekara ta hijira shamsiya kuma a tarjama wannan fim din ta Maryam (K).

386637