IQNA

An Yi Kira Zuwa Ga Zanga-Zanga Kan Gayyatar Wilders A Jamus

13:14 - October 02, 2010
Lambar Labari: 2005359
Bangaren kasa da kasa; An yi kira zuwa ga zanga-zanga nuna rashin amincewa da gayyatar Geert Wildes dan majalisar kasar Holland mai tsananin kyamar addinin muslunci zuwa kasar Jamus domin gabatar da jawabi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar zaman ta kasar Turkiya an bayyana cewa, an yi kira zuwa ga zanga-zanga nuna rashin amincewa da gayyatar Geert Wildes dan majalisar kasar Holland mai tsananin kyamar addinin muslunci zuwa kasar Jamus domin gabatar da jawabi a kasar ta Jamus.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan goron gayyata daya daga cikin tsoffin wakilan majalisar dokokin kasar ta Jamus ne mai tsananin gaba da addinin muslunci ya aike da goron gayyata Geert Wilders domin ya ziyarci Jamus tare da gabatar da jawabi na kiyayya da muslunci.

Wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar Jamus sun yi kira da a gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da gayyatar mutumin dan kasar Holland, da kuma hana shi gabatar da jawabi.

666510


captcha