Bangaren kasa da kasa;Kurbankali Burdi Muhammad Uf shugaban kasar Turkimanistan ya ziyarci gidan ajiyar kayan tarihi na Musulunci a kasar Katar kuma akwai manyan jami'an gwmanti da ke yi masa rakiya a cikin tawagar da ke yi masa rakiya.
Kamfanin dillancin labarai Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ta nakalto daga majiyar jaridar Katari ta Raya ta watsa rahoton cewa; Kurbankali Burdi Muhammad Uf shugaban kasar Turkimanistan ya ziyarci gidan ajiyar kayan tarihi na Musulunci a kasar Katar kuma akwai manyan jami'an gwmanti da ke yi masa rakiya a cikin tawagar da ke yi masa rakiya. Shugaban kasar da tawagar da ke yi masa rakiya sun gamsu da yadda aka nuna masu abubuwa daban-daban na fashar Musulunci da kuma na ilimi .
673435