IQNA

Kungiyar Hadin Kan Majalisun Musulunci Sun Yi Allah Wadai Kan Danganta Musulunci Da Ta'addanci

12:39 - October 26, 2010
Lambar Labari: 2020061
Bangaren kasa da kasa; kungiyar hadin kan majalisun dokokin na kasashen musulmi mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta fitar da wata sanarwa da a cikinta suka yi Allah wadai da rayawar siyasa da wasu kafafen watsa labarai da ke danganta ayyukan ta'addanci da addinin Musulunci.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna mai kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga jaridar hadeddiyar daular larabawa ya watsa rahoton cewa; kungiyar hadin kan majalisun dokokin na kasashen musulmi mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta fitar da wata sanarwa da a cikinta suka yi Allah wadai da rayawar siyasa da wasu kafafen watsa labarai da ke danganta ayyukan ta'addanci da addinin Musulunci.Wannan sanarwa ta z one bayan taron da komitin zartarwa na kungiyar majalisun kasashen musulmi suka gudanar da birnin Abu Zabi fadar mulkin hadeddiyar daular larabawa suna yin Allah wadai da duk wani mataki na cin fuska da muzanta gurare da abubuwea masu kima da daraja da daukaka na Musulunci kuma rashin adalci ne da neman haddasa fitina da zalunci kan addinin Musulunci da danganta duk wani aiki assha da ta'addanci da Musulunci.



682265

captcha