IQNA

Zaman Taro Kan Harkokin Saka Hannayen Jari A Mahanagar Musulunci A Tunisia

14:22 - February 20, 2011
Lambar Labari: 2083968
Bangaren kasa da kasa, Za a fara gudanar da zaman taro da zai yi dubi kan harkokin tattalin arzikin musulunci da kuma batun saka hannayen jari a mahanga ta addinin musulunci, wanda za a gudanar a karo na uku a birnin Tunis fadar mulkin kasar Tunisia.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na islamicbanking.ru an bayyana cewa, za a fara gudanar da zaman taro da zai yi dubi kan harkokin tattalin arzikin musulunci da kuma batun saka hannayen jari a mahanga ta addinin musulunci, wanda za a gudanar a karo na uku a birnin Tunis fadar mulkin kasar Tunisia a cikin watanni biyu masu zuwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar Tunisia da kuma wasu daga cikin kasashen mjsulmi da na larabawa, da kuma wasu kasashen duniya, domin duba hanyoyin karfafa juna a bangarorin ayyuka na harkokin tattalin arziki bisa ka’idoji na addinin musulunci.
Haka nan kuma zaman taron zai yi dubi kan lamurra da suka danganci saka hannayen jari a kamfanoni na kasashen musulmi , musamman ma wadanda suke karkashin tsarin nan na bankin musulunci da aka fara gudanarwa a wasu kasashen musulmi.
Za a fara gudanar da zaman taro da zai yi dubi kan harkokin tattalin arzikin musulunci da kuma batun saka hannayen jari a mahanga ta addinin musulunci, wanda za a gudanar a karo na hudu a kasar Tunisia.
750240

captcha