IQNA

Bayyana Wa Al'ummomin Kasashen Yamaci Hakikanin Musulunci Aiki Na Masana Musulimi

19:14 - March 09, 2011
Lambar Labari: 2093383
Bangaren kasa da kasa, Babban malamin kasar Ukraine Ahmad Tamim ya bayyana cewa, babban aikin da ya rataya kan masana musulmi a wanna zamanin ne su isar da sakon Musulunci na hakika ga al'ummomin kasashen yammacin turai, wadanda ba su da wata masaniya kan Musulunci da koyarwasa illa abin da makiya suka sanar da su.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labarai na gabacin turai an bayyana cewa, babban malamin kasar Ukraine Ahmad Tamim ya bayyana cewa, babban aikin da ya rataya kan masana musulmi a wanna zamanin ne su isar da sakon Musulunci na hakika ga al'ummomin kasashen yammacin turai, wadanda ba su da wata masaniya kan Musulunci da koyarwasa illa abin da makiya suka sanar da su kan mummunar akidar kyamar Musulunci da kuma mabiyansa.
Malamin ya ci gaba da cewa, sau da yawa wasu daga cikin al'ummomin kasashen turai suna gaba da Musulunci ne saboda abin da ake bayyana musu dangane da shi, amma ba don suna da wata masaniya kansa, kuma da a ce za su samu msaniya ta hakika kan sa mahanrsu da tunaninsu zai canja kan addinin Musulunci, bil hasali ma hakan zai sa wasunsu suka karbi Musulunci.
Babban malamin kasar Ukraine Ahmad Tamim ya bayyana cewa, babban aikin da ya rataya kan masana musulmi a wanna zamanin ne su isar da sakon Musulunci na hakika ga al'ummomin kasashen yammacin turai, wadanda ba su da wata masaniya kan Musulunci da koyarwasa illa abin da makiya suka sanar da su.
758180



captcha