Bangaren nazari da ilimi: a karo na hudu an gudanar da taron kasa da kasa kan musulunci addinin sulhu da fahimtar juna da aka gudanar a ranekun hudu da biyar ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a daidai lokacin tunawa da Ahmad haji Qadirov tsohon firaministan Ceceniya kuma an gudanar da taron ne a garin Grozni babban birnin wannan kasa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; a karo na hudu an gudanar da taron kasa da kasa kan musulunci addinin sulhu da fahimtar juna da aka gudanar a ranekun hudu da biyar ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a daidai lokacin tunawa da Ahmad haji Qadirov tsohon firaministan Ceceniya kuma an gudanar da taron ne a garin Grozni babban birnin wannan kasa. Wannan taro karawa juna ilimi an samu halartar wakilai daga kasashe kimanin talatin day a hada wakilan kungiyoyin addini da mazhabobi daban daban dam asana harkokin ilimi da malaman addini day an siyasa da suka fito daga kasashe irin su Koweiti,Labanon,Marooko,Suriya,Filipine,Chadi,Ostriya, Jamus, Krurwasiya, Azarbaijan,Bilarus,Kazakistan,Uzbakistan,Yukirain da sauran kasashen duniya.
799482